Mutum 4 sun mutu, 16 sun ji rauni a hatsarin mota a Bauchi

Hatsarin ya afku ne a sanadiyyar ɗaukar fasinjoji fiye da kima da direban motar ya yi.

Mutum 4 sun mutu, 16 sun ji rauni a hatsarin mota a Bauchi

Motar Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC)

Mutum huɗu sun rasu sanadiyyar hatsarin mota a garin Jalam da ke Ƙaramar Hukumar Dambam ta Jihar Bauchi.

Hatsarin wanda ya jikkata mutum 16 ya afku ne a daidai garin Dutsin Hari da ke kan hanyar Jalam zuwa Lanzai a Ƙaramar Hukumar Darazo.

Wasu shaidu sun ce hatsarin ya afku ne a sanadiyyar ɗaukar fasinjoji fiye da kima da direban motar ya yi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an garzaya da mutum 9 daga cikin waɗanda suka jikkata asibitin garin Jalam, yayin da aka miƙa biyar Babban Asibitin Danbam sai kuma mutum biyu da suka samu mummunan rauni an miƙa su Asibitin Azare.

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta bakin kakakinta, Mohammed Ahmed Wakil ta tabbatar da faruwar hatsarin.

SP Wakil ya bayar da sunayen mutum huɗun da aka tabbatar rasuwarsu a asibiti da suka haɗa da A’ishatu Salihu mai shekaru 25, Furera Haladu mai shekaru 25, Zuwaira Dandija mai shekara 19, and Lahala Muhammed mai shekaru 41.

Shi ma kakakin ’yan sandan ya alaƙanta afkuwar hatsari da gudun da ya wuce ka’ida da kuma ɗaukar fasinjoji fiye da kima da ke kan hanyar zuwa cin kasuwa a Ƙaramar Hukumar Darazo.

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza