Mutum 4 sun mutu, 59 sun jikkata a hatsarin mota a hanyar Abuja
Hatsarin ya faru ne sakamakon daukar lodi fiye da kima.
Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum hudu, sannan wasu 59 sun ji rauni sakamakon hatsarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kwamandan hukumar a jihar, Kabir Nadabo, ya ce hatsarin ya ritsa ne da wata tirela mai lamba MKA 99YS a kauyen Sabon Sara da misalin karfe 03:30 na safiyar Talata.
- An sace tsohon ciyaman da wasu mutum 10 a Taraba
- An binne mutum 8 da ’yan bindiga suka kashe a Katsina
Nadabo ya ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa, binciken farko ya nuna daukar lodin kaya da mutane da fiye da kima ce musabbabin hatsarin.
A cewar Nadabo, “Binciken ya nuna mutum 73 ne a cikin motar, 59 kuma sun samu raunuka, hudu sun mutu.”
Ya ce an kai wadanda suka jikkata asibitocin St. Gerard da AP Smart, da ke Kakuri.
Nadabo ya yi kira da babbar murya ga masu ababen hawa su gujin tukin ganganci da daukar lodi fiye da kima.
“Don haka, daga yanzu duk direban da aka kama da lodin kaya da mutane, za a gurfanar da shi a gaban kotu da laifin jefa rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya cikin hatsari.
“Yanzu haka mun kama direban tirelar da ya yi sanadin aukuwar wannan hatsarin,” in ji shi.