Mutum 4 sun mutu a hatsarin jirgin sama a Croatia

Ana ci gaba da neman wasu mutum biyu da ake zargin sun ɓace bayan hatsarin.

Mutum 4 sun mutu a hatsarin jirgin sama a Croatia

Mutum huɗu sun rasa rayukansu bayan wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari a kusa da wani filin saukar jirage da ke gaɓar tekun Adriatic a arewacin ƙasar Croatia.

’Yan sanda sun ce hatsarin ya auku ne a ranar Alhamis a yankin Campanoz da ke kusa da garin Medulin a yankin Istria, inda jami’an agaji suka garzaya wurin domin gudanar da aikin ceto.

Rahotanni sun ce ana ci gaba da neman wasu mutum biyu da ake zargin sun ɓace bayan hatsarin.

Hukumar kashe gobara ta ƙasar ta tabbatar da cewa jami’anta tare da ma’aikatan lafiya suna wurin da lamarin ya faru domin gudanar da ayyukan ceto da bincike.

Kamfanin watsa labarai na gwamnatin Croatia (HRT) ya ruwaito cewa jirgin, wanda ke ɗauke da rajistar Jamus, ya tashi ne daga ƙasar Austria zuwa Medulin kafin ya yi hatsarin.

An kuma ce jami’an hukumar binciken hatsarurrukan sufurin jiragen sama, ruwa da jiragen ƙasa ta Croatia na kan hanyarsu zuwa wurin domin gano musabbabin aukuwar lamarin.