Mutum 4 sun mutu a karon-battar ’yan sanda da masu garkuwa da mutane

A ranar Talata ’yan sanda suka rasa jami’insu daya kuma suka kashe wadansu masu garkuwa da mutane 2 a yankin karamar Hukumar Ikot-Ekpene da ke Jihar Akwa Ibom.  Lamarin ya auku ne kuwa a yayin da suka yi arangama da su a lokacin da suke kokarin kubutar da tsohon shugaban karamar hukumar mai suna Osen […]

Mutum 4 sun mutu a karon-battar ’yan sanda da masu garkuwa da mutane
Mutum 4 sun mutu a karon-battar ’yan sanda da masu garkuwa da mutane

A ranar Talata ’yan sanda suka rasa jami’insu daya kuma suka kashe wadansu masu garkuwa da mutane 2 a yankin karamar Hukumar Ikot-Ekpene da ke Jihar Akwa Ibom.  
Lamarin ya auku ne kuwa a yayin da suka yi arangama da su a lokacin da suke kokarin kubutar da tsohon shugaban karamar hukumar mai suna Osen Okene, wanda aka sace a ’yan makonnin da suka wuce, kodayake shi ma an kashe shi a lokacin arangamar.
Arangamar dai ta kai tsawon awoyi da dama, ana ta ba-ta-kashi a wani kauye da ke kusa da Ikot-Ekpene din, inda suka kashe wanda suke garkuwar da shi a yayin da suka ankara cewa’yan sandan sun kusa kaiwa gare su a dajin da suka tsare shi.
Jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan jihar, Mista Etim ya tabbatar da aukuwar lamarin.