Mutum 4 sun mutu a rikicin Fulani da kabilar Numana
An kashe mutum hudu tare da jikkata biyu a wasu hare-hare biyu da aka kai a rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa tsakanin Fulani da kabilar Numana, a garuruwan Ninte da Gada-Biyu da ke yankin Godogodo a karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna.A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan kabilar Numana […]
An kashe mutum hudu tare da jikkata biyu a wasu hare-hare biyu da aka kai a rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa tsakanin Fulani da kabilar Numana, a garuruwan Ninte da Gada-Biyu da ke yankin Godogodo a karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna.
A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan kabilar Numana suka zargi Fulani da kai harin da ya janyo asarar ran wata mace tare da jikkata mijinta da mahaifiyarsa a wani kwanton bauna da suke zargin Fulanin da yi lokacin da mutanen suke dawowa daga gona.
Mista Taru Barau, wanda aka kashe matarsa kuma ya tsira da harbin bindiga a cinyarsa, ya shaida wa wakilinmu a gadon asibiti cewa maharan, wadanda suke rufe da fuskokinsu sun labe ne a cikin dajin suka yi musu kwanton bauna “Muna tafe a kan babur mun taso daga gona ni da matata da mahaifiyata muna tsakar tafiya ba mu ankara ba, kawai sai mu ka ji karar bindiga. Na yi kokarin kubutar da mu amma da yake mata ne sai suka fado kasa, harsashi ya sami mahaifiyata a muka-muki ita kuma matata suka rufar mata da duka nan take ta mutu, ni ma kawai sai na ji harbin harsashi a cinyata da kyar na yi ta kici-kici da babur din har Allah Ya kubutar da ni,” inji shi.
Dagacin Ninte, Mista Hassan Jatau ya shaida wa Aminiya cewa wannan abin bakin ciki ya faru ne a daidai lokacin da suke zaman sulhu da shugabannin Fulanin a garin Zankan tare da Hakiman Jagindi da Zankan da Godogodo.
Ya ce, “Bayan Sakataren kungiyar CAN ya gama karanta takardar yarjejeniyar kowa ya yarda kuma ya sa hannu, ba a watse daga taron ba kawai sai aka kira waya aka ce ga abin da ke faruwa.”
Dagacin ya ce sau hudu ke nan in suna gabatar da zaman sulhu da Fulani amma haka na faruwa inda ya yi kiran a yi bincike sosai don gano marasa son zaman lafiya da ke haddasa rikicin kuma a samar musu da jami’an tsaro na dindindin a yankin.
Hari na biyuda aka kai kauyen Gada-Biyu da ke kusa da Ninte, an kai shi ne ranar Talata da safe inda mutanen garin suka ce suna zamansu sai suka ga mutane dauke da bindigogi sun fara bude musu wuta. Tanko Yakubu daya daga cikin matasan da suka sha da kyar kuma suka yi gudun hijira zuwa garin Godogodo, ya bayyana wa wakilinmu cewa, “Muna zaune da safe, sai muka ga mutane dauke da bindigogi sun fara bude mana wuta sai muka fita da gudu, Allah Ya taimaka akwai wadansu ’yan sandan kwantar da tarzoma biyu, a garin suka yi musayar wuta da su har Allah Ya sa suka kora su, amma kafin nan sun kashe danladi Gunta da Mamman Bala sai Friday Ali Numana cikon na uku.” Ya ce su babu abin da ya taba hada su da Fulani a garin.
A ranar Talatar wadansu mata dauke da ganyayyaki sun yi zanga-zanga zuwa fadar Sarkin Godogodo da ke garin Antang inda suka datse titin zuwa Jos don nuna rashin yardar da abin da suka kira Fulani na karkashe musu maza da kuma yi wa mata fyade.
Misis Deborah Daniel, daya daga cikin shugabannin zanga-zangar, ta shaida wa Aminiya cewa sun gaji da abin da Fulani ke yi musu a garuruwan Ninte da Gada-Biyu da Agwam da Golkofa na yi wa mata fyade don haka ta bukaci gwamnati ta kai musu sojoji yankin.
Shugabar Mata ta kungiyar CAN ta Gundumar Godogodo, Misis Deborah Reuben, ta ce sun fito ne domin nuna damuwarsu kan cin zarafin da ta ce Fulani na yi wa matansu ciki har da yi wa tsofaffi fyade. Ta ce sun sadaukar da kansu sun zabi Jam’iyyar APC saboda ganin ana yawan zubar da jini a gwamnatin PDP, amma sai ga shi a yanzu ne ake zubar da nasu jinin kuma ba abin da gwamnati ta yi.
Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a Kudancin Kaduna, Malam Abdulhamid Musa, ya shaida wa Aminiya cewa su ma haka suke jin wannan mummunan aiki ne kawai na ’yan ta’adda amma babu wata kwakkwarar hujja ta cewa Fulani ne ke aikata hakan tunda babu wanda aka kama sai dai zargi kawai. Don haka ya bukaci a daina dora wa Fulani laifi ko huce fushi a kansu. Ya ce sun samu labarin mata masu zanga-zangar sun kashe wan yaron Fulani a kusa da makabartar Antang inda suka ji wa daya rauni.
Aminiya ta samu labarin cewa kabilun Numana sun kokkone rugagen Fulanin da ke garuruwan Gada-Biyu da Golkofa. Kuma zuwa lokacin hada wannan rahoto gawa uku ’yan sanda suka kai dakin ajiye gawarwaki na Babban Asibitin Kafanchan.