Mutum 4 Sun Mutu Wasu Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Abiya

Akalla mutum hudu ne suka mutum a lokacin da babbar motar dakon kaya ta yi awon gaba da wata bus da Keke NAPEP.

Mutum 4 Sun Mutu Wasu Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Abiya

Hatsarin mota (Tsohuwar ajiya)

Akalla mutum hudu ne suka mutum a lokacin da babbar motar dakon kaya ta yi awon gaba da wata bus da Keke NAPEP.

Al’amarin ya faru ne a ranar Talata a kan gadar Ogbor-Hill da ke garin Aba a jihar Abia, lokacin da burkin babbar motar dakon kayan ya shanye.

Rahotanni sun ce bayan faruwar hadarin, mutane sun rika fito da fasinjojin ababen hawan da babbar motar ta take, sai dai baya ga wadanda suka rasu, akwai karin mutane da dama da suka samu munanan raunuka.

Wani ganau ya ce ‘mun rika ciro mutanen ne saboda babu motar janwe da za a yi anfani da ita wajen fito da ababen hawan da ke karkashin babbar motar.’

An hango Jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa FRSC a wajen da abun ya faru.

Ɗan shekara 43 ya auri mai shekara 88

Yadda ƙananan yara ke zaman kurkuku ba tare an da kai su kotu ba

PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun

Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu