Mutum 4 sun rasu, an ceto 19 a hatsarin kwale-kwale a Sakkwato
Sai dai jami’in ya ce har yanzu ana neman mutum ɗaya wanda ya ɓace.
Aƙalla mutum huɗu ne suka rasu a wani hatsarin kwale-kwale a yankin Dundaye da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko a Jihar Sakkwato.
Alhaji Aliyu Kafindangi daga Ofishin Gudanarwa na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) a jihar ne, ya tabbatar hakan a ranar Talata.
- Gwamnatin Tarayya za ta sa Almajirai 11,000 a makaranta
- ’Yan Najeriya na mutuwa saboda manufofin Tinubu – Ɗan Bello
Ya ce hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi.
Kafindangi, ya bayyana cewa an tura jami’an NEMA da sauran jami’an hukumomi wajen da hatsarin ya auku, inda suka gano gawar mutum huɗu a ranar Litinin.
Ya ce, hatsarin ya rutsa da mutum 24, amma an yi nasarar ceto mutum 19 da ransu.
A cewarsa an ɗauko gawar mutum ɗaya a ranar Lahadi, sannan a ranar Litinin aka sake samun gawar mutum uku, wanda ya kawo jimillar mutanen da suka rasu zuwa huɗu.
Sai dai ya ce har yanzu akwai mutum guda ɗaya da ake nema, yayin da ake ci gaba da bincike a yankin.
Jami’in na NEMA ya gode wa gwamnatin Jihar da kuma al’umma kan goyon bayan da suka ba su a lokacin da ake gudanar da aikin ceton.