Mutum 4 sun rasu a turmutsitsin rabon zakka a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin.

Mutum 4 sun rasu a turmutsitsin rabon zakka a Bauchi

Akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu a wajen turmutsitsin rabon zakka a Jihar Bauchi.

Lamarin ya auku ne a kamfanin Shafa Holdings plc da ke kan titin Jos, ranar Lahadi da misalin karfe 10 na safe.

Wata mai suna Na’ima Abdullahi mai shekara 17, ta jikkata a wajen rabon zakkar, wanda yanzu aka kwantar da ita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Ahmed Wakili, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa ’yan sandan sun ziyarci wajen bayan faruwar lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan ya bukaci mutane su kasance masu hakuri a duk lokacin da wani abu ya faru.

’Yan sanda sun tarwatsa dandazon jama’a da ke wajen domin karbar zakka, tuni rundunar ta jibge motocin dakarunta domin tabbatar da tsaro a yankin.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da kamfanin ya fitar game da faruwar lamarin.