Mutum 40 sun bace bayan kifewar kwalekwale a Kebbi

kwalekwalen yana dauke da mutane 50 a lokacin da ya yi hatsari a kan Kogin Neja

Mutum 40 sun bace bayan kifewar kwalekwale a Kebbi

Masu aikin ceto bayan kifewar wani jirgin ruwa a Jihar Kebbi a shekarar 2021

Kimanin mutum 40 ne ake zullumin sun bace bayan wani hatsarin kwalekwale a yankin Karamar Hukumar Yauri a Jihar Kebbi.

Aminiya ta gano cewa kwalekwalen ya yi hatsari ne yayin da yake dauke da kaya da fasinjoji kimanin 50 a kan Kogin Neja a rnaar Litinin.

Shugaban Karamar Hukuumar Yauri, Alhaji Bala Mohammed, ya ce fasinjojin da kwalekwalen sun taso ne daga kauyen Kasabo a Karamar Hukumar Agura na Jihar Neja a hanyarsu ta zuwa Yauri inda suka yi hatsari.

Ya ce hatsarin kwalekwale ya auku ne sakamakon karfin igiyar ruwa, kuma mutum 10 ne aka yi nasarar cetowa zuwa lokacin da muka samu wannan rahoto.

Amma ya ce “ana cii gaba da aikin ceto” da fatan sauran ma za a same su da ransu.

Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara

Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro