Mutum 42 sun halaka an kuma kone gidaje 200 a hare-haren Jihar Filato

Mutum 37 ne wasu mahara suka halaka a ranar Talatar da ta gabata a kauyukan Katu Kapang da Daron da Tul da Raruwu da suke kananan hukumomin Barikin Ladi da Mangu da ke Jihar Filato, wannan hari ya zo bayan harin da wasu da ake kyautata zaton ’yan kabilar Tarok suka kai kauyen Kaku da […]

Mutum 42 sun halaka an kuma kone gidaje 200 a hare-haren Jihar Filato
Mutum 42 sun halaka an kuma kone gidaje 200 a hare-haren Jihar Filato

Mutum 37 ne wasu mahara suka halaka a ranar Talatar da ta gabata a kauyukan Katu Kapang da Daron da Tul da Raruwu da suke kananan hukumomin Barikin Ladi da Mangu da ke Jihar Filato, wannan hari ya zo bayan harin da wasu da ake kyautata zaton ’yan kabilar Tarok suka kai kauyen Kaku da ke karamar Hukumar Shendam inda suka kashe mutum biyar tare da raunata mutane da dama da kuma kone sama da gidaje 200 da masallatai 20 a safiyar Asabar da ta gabata.
Wata sanarwa da ta fito daga kakakin rundunar STF Kyaftin Salisu Mustapha ta ce kimanin mutum biyar sun samu rauni a harin na ranar Talata, inda ya ce jami’ansu sun kai dauki cikin gaggawa zuwa yankin, sai dai kafin su isa maharan sun gudu. Ya ce al’amura sun lafa a yankunan.
Aminiya ta samu labarin cewa, an ga kansunan harsasai da kuma wuraren da suka huda a jikin gidaje. Dagacin Katu Pam Gyan Tsok ya shaida wa manema labarai cewa an kai harin ne da misalin karfe 1:00 na dare. Kuma ya ce maharan kwararrun makasa ne saboda suna magana ne da gangariyan Turanci.
A can yankin Shendam wani mazaunin kauyen Kaku da aka kai wa hari mai suna Attahiru Muhammad Rangmen ya shaida wa manema labarai cewa maharan da yawansu ya kai 300, sun isa kauyen ne dauke da manyan bindigogi da misalin karfe 5:00 na asuba, inda suka yi ta harbe-harbe da kone gidaje.
Ya ce, “Muna zaune sai muka ji karar harbe-harbe ta kowane bangaren garin, daga nan kowa ya kama gudu yana neman mafaka. Ya ce mutanen da aka kashe a harin sun hada da Abdullahi Dungu da Alhassan Audu kuala da Malam Inuwa danbakuwa da kuma Yakubu. Haka kuma an raunata mutane da dama tare da kona gidaje sama da 200 da masallatai 20.” Ya ce jami’an tsaro daga Jihar Taraba da ke makwabta da jihar ne suka zo suka kori maharan.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kashe mutum biyar a harin.
Kakakin Rundunar tsaro (STF) da ke aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato Kyaftin Salihu Mustapha ya tabbatar da faruwar harin.