Mutum 45 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Neja

Motar ta kama da wuta yayin da ta kife a ƙasa.

Mutum 45 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Neja

Aƙalla mutum 45 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya auku a kan titin Agaie zuwa Bida a Jihar Neja.

Hatsarin ya faru ne tsakanin wata tankar man fetur da wata motar dakon shanu, da kuma wata mota ɗauke da fasinjoji.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a kusa da ƙauyen Man-Woro da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Lahadi.

Motar dakon shanun ta taso ne daga Wudil da ke Jihar Kano, yayin da ta ke kan hanyarta na zuwa Legas, yayin da ɗaya motar ɗauke da fasinjoji ke kan hanyarta zuwa kasuwar Lahadin Agaie.

Wani mazaunin yankin, Abubakar Agaie, ya bayyana cewa an birne gawarwakin mutum 45 a ƙauyen Man-Woro da safiyar ranar Lahadi.

Wani direban mota, Alhaji Wuchiko, ya ce ya kai direban tankar da wani wanda ya jikkata zuwa Babban Asibitin Lapai, yayin da wasu da suka tsallake rijiya da baya aka kai su Asibitin Koyarwa na Tarayya, da ke Bida.

An ce hatsarin ya faru ne yayin da tankar man ta kife yayin da ta ke ƙoƙarin kaucewa ramuka a kan hanyar.

Wani ganau, Yahaya Mohammed, ya ce sun lissafa gawarwakin aƙalla mutum 45, sai dai ya ce duk sun ƙone ƙurmus.

“Motoci ukun sun ƙone gaba ɗaya. Lokacin da tankar ta kife ta kama da wuta, motar fasinjojin da motar ɗaukar kaya da mutane sun yi ƙoƙarin kaucewa, amma sai da suka faɗa cikin wutar,” in ji shi.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), ta tabbatar da mutuwar sama da mutum 30, tare da shanu fiye da 50 da suka ƙone ƙurmus.

Jami’an hukumar sun ci gaba da aikin ceto a wajen da hatsarin ya auku, inda suke ƙoƙarin ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin motocin.

Gwamna Mohammed Umaru Bago, ya nuna alhininsa game da hatsarin.

Ya kuma aike tawagar agaji zuwa wajen da hatsarin ya auku.

Ya yi kira ga jama’a da su kasance masu yin taka-tsan-tsan, tare da bin dokokin hanya don kauce wa irin wannan hatsari.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar nema wa waɗanda suka jikkata lafiya.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka