Mutum 45 sun mutu yayin bankwana da gawar Magufuli
Akalla mutum 45 ne suka rasa rayukansu a turmutsutsun bankwana da gawar tsohon Shugaban kasar Tanzania, John Magufuli. Rundunar ‘yan sandan kasar ta bakin wani babban jami’i, Lazaro Mambosasa ce ta tabbatar hakan a ranar Talata yayin da kuma ta ce an samu karin mutum 37 da suka jikkata a cunkoson da ya auku a […]
Akalla mutum 45 ne suka rasa rayukansu a turmutsutsun bankwana da gawar tsohon Shugaban kasar Tanzania, John Magufuli.
Rundunar ‘yan sandan kasar ta bakin wani babban jami’i, Lazaro Mambosasa ce ta tabbatar hakan a ranar Talata yayin da kuma ta ce an samu karin mutum 37 da suka jikkata a cunkoson da ya auku a Dar es Salaam, babban birnin Kasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Andalou ya ruwaito cewa, jami’an ‘yan sanda ba su bayyana sunayen wadanda suka riga mu gidan gaskiya ba.
Hakan na zuwa ne a yayin da aka yi wa mahukunta matsin lambar bayyana hakikanin asarar rayuka da cunkoson ya haddasa.
A baya can an sanar da mutuwar mutum biyar kacal, inda bayan mako daya da faruwar lamarin wani dangi suka bayyana cewa ‘yan uwansu shida ne suka mutu a turmutsutsun.
A ranar 26 ga watan Maris aka yi jana’izar marigayi Magufuli a cibiyarsa ta garin Chato bayan rasuwarsa a ranar 17 ga watan yana da shekara 61 a doron kasa.
Aminiya ta ruwaito cewa, mataimakiyar marigayi Magufuli, Samia Suluhu Hassan ce aka rantsar a matsayin mace ta farko da za ta jagoranci kasar a tarihi.