Mutum 452 sun kara kamuwa da coronavirus a Najeriya
Hukumar Yaki da Cututttuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce yawan masu cutar coronavirus a kasar ya karu zuwa 21,371 bayan karin mutum 452 sun kamu da cutar a ranar Laraba 23 ga watan Yuni. Alkaluman cutar da NCDC ta fitar ranar sun nuna yawan wanda cutar ta yi ajalinsu ya karu zuwa 533, […]
Hukumar Yaki da Cututttuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce yawan masu cutar coronavirus a kasar ya karu zuwa 21,371 bayan karin mutum 452 sun kamu da cutar a ranar Laraba 23 ga watan Yuni.
Alkaluman cutar da NCDC ta fitar ranar sun nuna yawan wanda cutar ta yi ajalinsu ya karu zuwa 533, yayin da wasu 7,338 suka warke.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta nuna an samu karuwar mutum 209 a jihar Legas inda aka fara samun bullar cutar a watan Fabrairu, kuma inda ta fi kamara.
- Najeriya ta samu kyautar inji mai gwajin coronavirus 3,000 a rana
- ’Yar shekara biyu ta kamu da coronavirus
A ranar kuma mutum 67 sun kara kamuwa a jihar Delta, yayin da a Abuja aka samu karin mutum 22.
Jihar Abia na da sabbin mutum 20, sai Inugu mai mutum 16 yayin da jihar Bauchi aka samu karin mutum 15.
Jihohin Kaduna da Ondo kowannensu ya samu karin mutum 8, jihar Osun mutum 7, an kuma samu mutum uku-uku a Imo da Binuwai, a Bonro kuma mutum daya.