Mutum 4600 za su sauke farali bana daga Jihar Katsina

Babban Daraktan Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina Alhaji Muhammadu Abu Rimi, ya ce akalla maniyata aikin Hajji 4,622 ne ake sa ran su sauke farali bana daga jihar a yayin aikin Hajjin bana da za a fara jigilar maniyyatan a ranar Litinin mai zuwa. Alhaji Muhammadu Abu Rimi ya shaida wa manema labarai haka ne […]

Mutum 4600 za su sauke farali bana daga Jihar Katsina
Mutum 4600 za su sauke farali bana daga Jihar Katsina

Babban Daraktan Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina Alhaji Muhammadu Abu Rimi, ya ce akalla maniyata aikin Hajji 4,622 ne ake sa ran su sauke farali bana daga jihar a yayin aikin Hajjin bana da za a fara jigilar maniyyatan a ranar Litinin mai zuwa.
Alhaji Muhammadu Abu Rimi ya shaida wa manema labarai haka ne a ofishinsa, inda ya ce, kusan kashi 95 daga cikin 100 na maniyatan sababbin zuwa ne. Ya ce, sun shirya taron bita na tsawon mako biyar ga maniyyatan a kan abin da ya shafi aikin Hajjin domin ganin an gudanar da aikin cikin nasara. “Kuma a bana mun kama wa alhazanmu masauki a inda suka saba sama da shekara 30 da suka wuce domin ganin cewa an samu saukin zirga-zirga sabanin abin da ya faru a bara. Mun kuma yi kokarin ganin ba mu rarraba alhazanmu zuwa wurare ba yadda za a rika samun matsala wajen gano masaukansu ganin cewa maniyatan na bana mafi yawansu sababbin zuwa ne,” inji shi.
Daraktan ya ce, tuni suka dauki fasfon maniyata sama da 3000 domin nemo musu biza kuma sun tanadi jirgin da zai dauki alhazan jihar. Sai ya ja hankalin maniyatan cewa kudin guzuri a bana akwai sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya ya bullo da shi a kan masu babbar kujera mai Dala 1500, inda ya ce, za a canja wa musu Dala daya kan Naira 197 har zuwa Dala dubu. Amma sauran dala 500 za a canja su ne bisa farashin da kasuwa ta nuna. Ya ce sauran kujerun kuwa duk za a canja musu ne a kan Naira 197 a kan kowace Dala.
Alhaji Abu Rimi ya ce, daga bana Saudiyya ba ta yarda kowace jiha ta fitar da wurin shan maganinta daban ba, duk abin da ya shafi kiwon lafiya yana karkashin Hukumar Hajji ta kasa ce sai dai kowace jiha za ta bayar da ma’aikatan kiwon lafiya da ba za su wuce bibbiyu ba.
Ya ce an ba Jihar Katsina damar tura ma’aikata 20, wato likitoci 8 da Nas-Nas 8 da masu bayar da magani 4.
Babban Daraktan ya yi kira ga maniyyatan jihar cewa, su rika fitowa a duk lokacin da suka ji an neme su. “Duk maniyyacin da bai fito a kan lokaci ba, ya tsaya zaben jirgi, in ya rasa jirgi sai dai ya jira wata shekarar ko ya jira hukuncin da hukuma za ta dauka a kan dalilin da ya bayar na rashin fitowarsa a kan lokaci. Har wayau, maniyyata su kiyaye dokokin da aka shimfida musu tun daga nan gida har zuwa kammala aikinsu,” inji shi.