Mutum 47 sun mutu a hadarin jirgin sama a Pakistan

Wani jirgin sama mallakar kamfanin Pakistan International Airlines (PIA) dauke da fiye da mutum 40 ya fadi a arewacin kasar. Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce jirgin, mai lamba PK-661, “ya daina samun bayanai daga jami’an kula da jirage a kan hanyarsa ta zuwa Islamabad daga Chitral”.Kafofin watsa labarai na Pakistan sun ambato […]

Mutum 47 sun mutu a hadarin jirgin sama a Pakistan
Mutum 47 sun mutu a hadarin jirgin sama a Pakistan

Wani jirgin sama mallakar kamfanin Pakistan International Airlines (PIA) dauke da fiye da mutum 40 ya fadi a arewacin kasar.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce jirgin, mai lamba PK-661, “ya daina samun bayanai daga jami’an kula da jirage a kan hanyarsa ta zuwa Islamabad daga Chitral”.
Kafofin watsa labarai na Pakistan sun ambato ‘yan sanda da kuma jami’ai na cewa jirgin ya fadi ne a kusa da garin Habelian, wanda bai da nisa da Arewacin Islamabad.
Yayin lokacin hada wannan rahoton, hukumomi sun ce ana amfani da dukkan ma’aikata da kayan aiki domin gano inda jirgin yake.
A baya an zargi kamfanin jiragen kasar da rashin kula da lafiyar jiragensa, inda mutum 44 suka mutu a wani hadari a shekarar 2006.
kungiyar Tarayyar Turai ta dakatar da jiragen kamfanin a 2007 saboda damuwa kan ingancinsu.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara