Mutum 5 da suka yi tashe a shafukan sada zumunta a 2024

Ɗan Bello da Rigi-Rigi da Bala Sarkin Marke suna daga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a Soshiyal Midiya a Shekarar 2024

Mutum 5 da suka yi tashe a shafukan sada zumunta a 2024

Kafofin sada zumunta a shekarar 2024 sun ɗauki hankalin jama’a sosai da abubuwa da dama.

A shekarar ce wasu ɗaiɗaikun mutane suka zo da irin nasu salon wanda hakan ya sa suka yi fice a tsakanin ma’abota shafukan.

Ɗan Bello zuwa Sheikh Rigi-Rigi zuwa Bala Sarkin Marke da sauransu, kaɗan ne daga cikin mutanen da suka yamutsa hazo a Soshiyal Midiya a shekarar.

Ga jerin wasu da muka rairayo muku:

1- Dokta Idris Dutsen Tanshi

Sheikh Dakta Idris Abdulazeez Duten Tanshi ɗaya ne daga cikin jerin mutanen da Aminiya ta gano cewa sun yi fice a kafafen sada zumunta a 2024 da muke bankwana da ita. Duk da cewa shehin malamin ya yi shuhura tun a baya sakamakon wasu ra’ayoyinsa da suka sha bamban da na mafi yawan mutane.

A bana malamin ya yi fice ne sakamakon turka-turkar da ta auku tsakaninsa da mahukunta a jihar Bauchi, lamarin da ta kai ga ya yi hijira har sai da ƙura ta lafa sannan ya dawo.

Kafin hijirar Sheikh Dutsen Tanshi, sai da Gwmanatin Jihar Bauchi ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin neman tayar da zaune tsaye. Zargin ya kai ga tsare malamin a gidan gyaran hali kafin daga baya kotu ta bayar da belinsa bayan ya shafe wata guda.

Daga nan ne kuma Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya ƙara jan hankalin mabiya musamman saboda irin kalaman da ya ke yi yayin gabatar da huɗubar Juma’a a kowane mako a masallacinsa.

An yi hasashen cewa ya zuwa yanzu shi ne malamin da matasa a shafukan sada zumunta suka fi bibiya kai-tsaye a Facebook inda yake watsa huɗubar kai tsaye.

2- Ɗan Bello:

Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Dan Bello ya yi fice wajen amfani da shafukan sada zumunta musamman TikTok wajen yaƙi da mummunan shugabanci da cin hanci tare da fafutikar samar da shugabanci na gari ta hanyar bidiyon barkwanci.

A shekarar 2024 Ɗan Bello ya fitar da wasu bidiyon fallasar cin hanci da sauransu waɗanda suka yamutsa hazo matuka, musamman ganin irirn zarge-zarge da ya yi a cikin bidiyoyin.

Wannan ya sa mutane da dama bibiyar sa domin ganin sabon bidiyon da zai fitar.

Ɗan Bello Bakano ne da ke zaune a Kasar Sin a halin yanzu inda ya ke aiki a matsayin malamin makaranta, kuma daga can ne yake samar da bidiyonsa.

3- Sheikh Rigi-Rigi:

Sheikh Usman Kusfa wanda ake wa laƙabi da Rigi-Rigi, wanda yanzu aka fi sani da Attalili Attagazuty, ɗaya daga cikin malaman Dariƙar Tijjaniyya da suka yi fice a wannan zamani. Rigi-Rigi ya ja hankalin mutane a shafukan sada zumunta da salonsa na musamman, ma yadda yake karantar da almajiransa jerin sunayen wasu sahabban Shehu Ahmadu Tijjani.

Kafofin sada zumunta da dama sun rawaito yadda Rigi-Rigi ya zo da sabon salo na karantarwa, inda mutane da dama musamman a TikTok suka riƙa kwaikwayon sa, duk da cewa da dama suna yi ne domin nuna ƙin amincewa da batutuwan da yake gabatarwa.

An rawaito cewa Sheikh Rigi-Rigi ya daɗe yana gabatar da karatuttuka tsawon lokaci mai tsawo, amma dai sai yanzu ne tauraronsa ya haska a tskannain matasan, musamman masu ta’ammali da shafukan sada zumunta. An rawaito cewa Sheikh Rigi-Rigi ya taɓa gwabza muƙabala da Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Allah Ya gafarta masa.

Rigi-Rigi ya samu lambobin yabo da dama daga wajen wasu mutane kan karatuttukansa da yake gabatarwa.

4- Bala Sarkin Marke

Wani mutum ɗan shekara 70 mai suna Bala Muhammed ɗan asalin jihar Bauchi wadda mutane ke wa lakabi da Bala Sarkin Marke a dandalin Facebook, shi ma ya tayar da ƙura aa kafofin sada zumunta a bana.

Hotunan Bala shi da tsofaffin ’yan mata iri-iri su kimanin 70 sun watsu a kafafen sada zumunta a tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwambar 2024. Hotunan sun nuna yadda Bala yake hutawa da ’yan matansa wanda yake ikirarin cewa idan dama ta samu dole a ɗan huta.

Sai dai Hukumar Hisbah ta Jihar Bauchi ta cafke shi inda ta tuhume shi da yaɗa hotunan a matsayin yaɗa alfasha tare da keta alfarmar matan da ya yi mu’amala da su.

Sai dai Bala ya ce yawancin hotunan ya ɗauke su ne sama da shekara 20 da suka wuce a lokutan da yake nishaɗi domin more rayuwarsa shi da ’yan matan nasa.

Ya ƙara da cewa yana lallamar matan ne ta hanyar hikima domin ya huta da su.

Bala ya ce bai taɓa aure ba, amma yanzu haka ya bazama neman matar da zai aura, amma sai wacce take da aikin yi domin kula da yaran da za ta haifa musu idan ya mutu.

A karshe bayan tuhumar da hukumar Hisba ta yi masa Bala ya bayar da haƙuri ga matan da ya yaɗa hotunansu inda ya ce shi bai yi hakan da niyyar tozarci ba, sai dai don hakan ’yancinsa ne na walwala.

5- Sheikh Salihu Alƙali Zariya

Sheikh Alkali Zariya shararren malami ne a shafukan sada zumunta musamman a shekarar 2024. Malam Salihu ya zo da sabon salo wanda ya sa ’yan TikTok musamman ’yan mata ke jin daɗin sauraro. Malamin yakan yi nasiha a kan batutuwa da suka shafi mu’amalar aure, zamantakewa da kuma kira ga shugabanni a kan samar da sauƙi daga halin da al’umma suke ciki a yanzu.

Wani dalili da ya sa malamin ya ƙara shahara a shafukan sada zumuntar shi ne, duk da yabo da yake yawan yi wa uwar gidansa da yake yawan ambato, wato Hajiya Jamila, wannan bai hana shi ƙara mata abokiyar zama ba, wanda hakan ba ƙaramin jan hankalin ma’ab

ota shafukan sada zumunta ya yi ba.