Mutum 5 sun kamu da cutar Kyandar Biri a Adamawa
Hukumomi a Jihar Adamama sun sanar da harbuwar mutum biyar da cutar Kyandar Biri.
Hukumomi a Jihar Adamama sun sanar da harbuwar mutum biyar da cutar Kyandar Biri.
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar ta ce kawo yanzu an tabbatar da mutum biyar sun kamu da cutar, akwai wasu 57 kuma da ake gudanar da bincike a kansu bisa zargin kamuwa da ita.
- Anderlecht na zawarcin dan wasan Najeriya Abdulrazak Ishaq
- Kotun Koli ta soke dokar haramta sanya hijabi a makarantun Jihar Legas
Daraktar Hukumar Lafiya ta Jihar Dokta Celine Laori ta ce an fara gano bullar cutar a jihar ce a watan Afrilu a barikin sojoji da kuma gidan yari da ke garin Yola.
Ta bayyana cewa an gano kwayar cutar ce a Karamar Hukumar Yola ta Arewa da kuma Yola ta Kudu ta Jihar.
“Tabbas an samu bullar cutar Kyandar Biri a Jihar Adamawa tun a wata Afrilu, kamar yadda Kwamishinan Lafiya ya sanar a lokacin da yake sanar da kawo karshen aikin yaki da cutar Kwalara.
Ta bayyana cewa, “Kwayar cutar da ke haddasa cutar Kyandar Biri tana kama da wadda take kawo cutar Kyanda.