Mutum 5 sun kone kurmus a gobarar tankar mai a Ogere
Tukin gangancin direban tankar mai ya haddasa hatsashi da tashin gobara.
Mutum biyar sun kone kurmus bayan wata tankar dakon mai ta yi bindiga a safiyar Laraba.
Tankar man ta kama da wuta ne bayan ta yi karo da wata motar dakon kaya a kusa da wani gidan mai a yankin Ogere, Jihar Ogun.
- Mutane da dama sun mutu bayan fashewar tankin iskar gas a Legas
- Kotu ta daure uba saboda yin lalata da ’ya’yansa a Gombe
“Mutum biyar sun kone kurmus ba za a iya gane su ba,” a cewar mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen jihar, Florence Okpe.
Ta ce, “An gano gawarwakin mutanen ne a cikin daya daga cikin motocin kuma an wuce da gawarwakin zuwa dakin ajiyar gawa da ke Ipara a Karamar Hukumar Remo ta Arewa ta jihar.”
Shaidu sun ce a sakamakon faruwar lamarin a kan babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta ne wutar ta kama mutum biyar din da “suka kone kurmus”.
Taho-mu-gama da motocin suka yi ke da wuya sai man da tankar take dauke da shi ya fara tsiyaya, wuta ta fara ci, har ta kama kama akalla mutum biyar.
Florence Okpe, ta ce “Tukin ganganci da kokarin wucewa ba bisa kai’ida ba da direban tankar man ke yi ne ya haddasa hatsarin.”
Ta kuma bayyana cewa akalla motoci biyar sun kone a sakamakon gobarar da ta tashi bayan motocin sun biyu sun yi karo.
Jami’ar ta ce tuni aka karkatar da akalar ababen hawa masu bin hanyar domin kawar da yiwuwar aukuwar wani hatsarin.
Idan ba a manta ba ranar Lahadi da dare wasu mutum bakwai suka kone kurmus a wani hatsarin mota a kan hanyar Legas zuwa Abeokuta.