Mutum 5 sun mutu, 37 sun jikkata a hatsarin mota a Koriya ta Kudu
Mutum 37 suka jikkata sakamakon hatsarin.
Yadda hayaki ya tarnake wurin da hatsarin ya auku
Rahotanni daga kasar Koriya ta Kudu sun ce akalla mutum biyar sun mutu, 37 sun jikkata a wani hatsarin mota da ya haifar da gobara.
Hukumomin kasar sun ce hatsarin ya auku ne a Seoul, babban birnin kasar, inda wata motar daukar kaya da wata bas, suka yi taho-mu-gama.
- Abun fashewa ya kashe mutum 4 A Fadar Sarki gabanin ziyarar Buhari a Kogi
- Hana mata aikin jinkai ta haifar wa MDD tsaiko a Afghanistan
Sai dai babu wani cikakken bayani kan abin da ya haifar da hatsarin na ranar Alhamis.
Majiyarmu ta ce hatsarin ya auku ne a babbar hanyar da ta bi ta bututu a Gwacheon da misalin karfe 1:50 na rana agogon kasar.
An ga hayaki ya turnuke inda iftila’in ya auku da kuma jami’an kwana-kwana suna kokarin kashe gobarar da ta kama.