Mutum 5 sun mutu wasu sun ɓace a kifewar kwale-kwale a Jigawa

Kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji 20 ya kife a Kogin Gamoda da ke kusa da ƙauyen Nahuce.

Mutum 5 sun mutu wasu sun ɓace a kifewar kwale-kwale a Jigawa

Mutum biyar ne suka mutu sakamakon haɗarin kwale-kwale a Ƙaramar Hukumar Taura da ke Jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne da tsakar ranar Alhamis yayin da kwale-kwalen da ke ɗauke da fasinjoji 20 ya kife a lokacin da suke tsallakawa kogin Gamoda da ke kusa da ƙauyen Nahuce.

A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Jigawa ta fitar, ta ce da samun wannan kiran na gaggawa, jami’an ‘yan sanda, da masu ruwa da tsaki sun garzaya wurin da lamarin ya faru domin ceto fasinjojin.

Amma “Abin takaici, an gano biyar daga cikin fasinjojin da suka mutu,” in ji kakakin rundunar ’yan sandan na Jigawa, Lawan Shiisu Adam.

Shiisu ta bayyana sunayen waɗanda abin ya shafa da suka haɗa da Abdurra’uf Mohd, mai shekara 15 da Suleman Ali mai shekara 20 da Shafiu Mohammad mai shekara 25 da Ado Nafance mai shekara 75 da kuma Alasan Mohammad mai shekara 16.

Jami’in ya ce duk waɗanda suka rasun ‘yan Ƙaramar Hukumar Taura ne.

Aminiya ta ruwaito Kwamishinan ‘yan sandan jihar Amad Abdullahi yana jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

“Muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan tare da roƙon Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu,” in ji shi.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume