Mutum 5 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Filato
Shugaban ya gargaɗi direbobi kan gudun wuce ƙima.
Aƙalla mutum biyar ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a shatale-talen Zangzat da ke Ƙaramar Hukumar Langtang ta Arewa, a Jihar Filato.
Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 3 na safiyar ranar Lahadi, inda wata babbar mota ɗauke da shinkafa da fasinjoji, wadda ta taso Shendam zuwa Jos ta yi hatsari.
- Najeriya na samun rarar N10bn duk shekara sakamakon cire tallafin man fetur– Sanata
- Mutane 25 sun mutu, 14 sun nutse a hatsarin jirgin ruwa a Yobe
Shugaban Ƙaramar Hukumar, Pirfa Jingfa Tyem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Ya kuma ce hatsarin ya auku ne sakamakon gudun wuce kima da ɗaukar kaya fiye da ƙima da motar ta yi.
Ya ƙara da cewa waɗanda suka ji rauni suna samun kulawa a Asibitin Gwamnati na Langtang.
Hukumar ta aike jami’anta zuwa wajen da hatsarin ya faru da kuma asibiti don taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
Shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.
Hakazalika ya gargaɗi direbobi da su guji gudu fiye da ƙima da ɗaukar kaya masu yawa don hana faruwar irin waɗannan hatsari a gaba.