Mutum 5 sun rasu, 8 sun jikkata a hatsarin mota a Oyo

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin ba su agajin gaggawa.

Mutum 5 sun rasu, 8 sun jikkata a hatsarin mota a Oyo

Aƙalla mutum biyar sun rasu nan take yayin da wasu takwas suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya auku a Ibadan, Jihar Oyo.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da faruwar hatsarin da yammacin ranar Juma’a a ƙauyen Guru-Mahraji, kusa da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Shugaban hukumar, Mista Maroof Akinwande, ya ce hatsarin ya shafi motoci da dama, ciki har da tireloli shida, tankokin gas biyu, mota ƙirar Hilux guda biyu da kuma wasu ƙananan motoci biyu.

Ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da birki ya ƙwace wa direban wata tirela, inda ya yi karo da wata tirela da ke tsaye a gefen hanya, abin da ya jawo sauran motocin suka riƙa karo da juna.

Sakamakon haka, mutum biyar sun mutu nan take, yayin da aka garzaya da wasu takwas asibiti.

Akinwande, ya kuma ce wuta ta tashi a wajen, amma jami’an kashe gobara sun yi saurin shawo kanta kafin ta bazu.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano musababbin aukuwar hatsarin.