Mutum 5 sun yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe

Wasu mutum uku sun shiga hannun hukuma kan zargin sun yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyade. ’Yan sanda sun kama mutanen ne bayan sun yi wa yarinyar aika-aikan a yankin Okpella da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas a Jihar Edo. Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Umoru Ozigi na ya sanar da haka a […]

Mutum 5 sun yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe

Wasu mutum uku sun shiga hannun hukuma kan zargin sun yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyade.

’Yan sanda sun kama mutanen ne bayan sun yi wa yarinyar aika-aikan a yankin Okpella da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas a Jihar Edo.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Umoru Ozigi na ya sanar da haka a lokacin da matar gwamna jihar, Misis Edesili Anani, ta ziyarce shi a ofishinsa.

Matar gwamnan ta yaba masa kan ɗaukar mataki cikin gaggawa bayan ɓullar bidiyon da masu fyaɗen suka ɗauka a yayin da suke wa yarinyar aika-aikan a ranar jajibirin Kirsimeti.