Mutum 55 kacal suka sace Naira tiriliyan 1.3 cikin shekara 7 – Ministan Watsa Labarai

Ministan wanda ya ce, an tafka wannan sata ce a karshen zangon mulkin Shugaba Obasanjo na biyu da kuma mulkin marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa da kuma Goodluck Jonathan, ya ce mutane 15 daga cikin wadanda ake zargin, tsofaffin gwamnonin wadansu jihohi ne, 4 kuma tsofaffin ministoci ne da kuma tsofaffin manyan ma’aikata a gwamnatocin tarayya […]

Mutum 55 kacal suka sace Naira tiriliyan 1.3 cikin shekara 7 – Ministan Watsa Labarai
Mutum 55 kacal suka sace Naira tiriliyan 1.3 cikin shekara 7 – Ministan Watsa Labarai

Ministan wanda ya ce, an tafka wannan sata ce a karshen zangon mulkin Shugaba Obasanjo na biyu da kuma mulkin marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa da kuma Goodluck Jonathan, ya ce mutane 15 daga cikin wadanda ake zargin, tsofaffin gwamnonin wadansu jihohi ne, 4 kuma tsofaffin ministoci ne da kuma tsofaffin manyan ma’aikata a gwamnatocin tarayya da na jihohi

 

A kokarin Gwamnatin Tarayya na binciken yadda aka wawure dukiyar gwamnati, an samu tabbacin cewa wadansu mutane 55 ne suka sace adadin Naira tiriliyan 1 da biliyan 3 a cikin shekara bakwai kacal, daga 2006 zuwa 2013.
Ministan Watsa Labarai da Raya Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata, a yayin wata ziyara ta musamman da ya kawo wa jaridar Aminiya a babban ofishinta da ke Abuja. Ya ce wannan adadin kudin sun haura kashi daya bisa hudu na kasafin kudin Gwamnatin Tarayya na bana.
Ministan wanda ya ce, an tafka wannan sata ce a karshen zangon mulkin Shugaba Obasanjo na biyu da kuma mulkin marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa da kuma Goodluck Jonathan, ya ce mutane 15 daga cikin wadanda ake zargin, tsofaffin gwamnonin wadansu jihohi ne, 4 kuma tsofaffin ministoci ne da kuma tsofaffin manyan ma’aikata a gwamnatocin tarayya da na jihohi. A yayin da kuma 8 daga cikinsu manyan ma’aikatan bankuna ne, sai kuma mutum 11 da suka kasance manyan ’yan kasuwa.
Ministan ya ce gwamnonin nan 15 sun sace kimanin Naira biliyan 146 da miliyan 84, tsofaffin ministocin su 4 suka wawure Naira biliyan 7. Su kuwa tsofaffin manyan ma’aikatan gwamnatocin tarayya da na jihohi su 12, sun sace kimanin Naira biliyan 14 ne, a yayin da manyan ma’aikatan banki su 8 suka sace Naira biliyan 524, sai kuma manyan ’yan kasuwa suka wafce Naira biliyan 653.
Da aka tambaye shi cewa, me zai hana ya bayyana sunayen wadannan mutane da ake tuhuma da sace wadannan kudi masu yawa haka, sai Mnistan ya ce: “Mutane da yawa suna kalubalantata, cewa in bayyana masu yadda aka yi na samu wannan bayani. Ni kuwa nakan gaya masu cewa ai wannan ba wani boyayyen bayani ne ba, domin abin da mutum ke bukata kawai idan yana son sanin hakikanin bayanin shi ne, ya je ya duba mutanen da hukumar EFCC ke gurfanarwa gaban kotuna daban-daban tsakanin shekarar 2006 zuwa 2013, zai samu sunayensu da kuma adadin kudaden da suka sace.”
Da yake nuna takaicinsa game da adadin kudin nan da aka sace, ministan ya bayyana cewa mutum 55 da ne kadai suka sace kudaden da ya kamata a ce an yi wa al’ummar kasa ayyukan raya kasa, wanda zai samar da hanyoyi da asibitoci da makarantu.
“Adadin kudin nan da aka sace, za su iya amfanar al’ummar Najeriya kamar haka: Za a iya samar da tagwayan hanyoyi masu inganci, masu tsawon kilomita 100 a kowace shiyyar Najeriya guda shida da muke da su. Za a iya gina manyan asibitoci na zamani masu kayan aiki ingantattu guda 36, wato kowace jiha za ta samu irin wannan asibiti guda daya. Za a iya gina ingantattun makarantu na zamani dauke da kayan aiki na zamani guda 183. Za a iya daukar nauyin karatun dalibai guda 3,974 tun daga firamare har jami’a, idan za a kashe wa kowane dalibi Naira miliyan 25 da dubu 24. Za kuma a iya gina ingantattun gidaje masu dakuna bibbiyu guda dubu 20 da guda 62, duk a cikin wadannan kudade da aka sace.” Inji shi, inda ya fusata da wasu ’ya’yan jam’iyyar adawa da suke nuna cewa bai kamata a binciki wadannan barayi ba.
Ministan kuma ya sha alwashin cewa gwamnatin nan ta Muhammadu Buhari ta sha alwashin tabbatar da canji mai amfani, inda ta daura gagarumin yaki da almundahana. Ya ce babu gudu babu ja da baya a kan wannan yaki, domin a cewarsa, duk wadanda ake tuhuma da sace kudin nan ba su musanta ba, sai dai suna ba da wasu guragun hujjoji.
“Babu abin da mutanen ne ke gindayawa a matsayin hujjarsu ta sace kudaden nan sai shirme da abin mamaki. Wani daga cikinsu cewa ya yi ya amshi Naira biliyan 4 da miliyan 5 a matsayin kudin yin addu’a. Wani kuma ya ce ya amshi Naira biliyan 2 da miliyan1 domin aikin watsa labarai, a yayin da wani kuma ya ce ya amshi Naira biliyan 13 domin ya biya kudin da aka sayin filin wata jami’a ta horar da sojojin ruwa. A yayin da muke samun wadannan bayanai, babu yadda za a yi mu rungume hannuwanmu, mu kyale su su sha da dukiyar al’umma.” Inji Minista Lai Mohammed.