Mutum 58 sun mutu a harin kunar bakin waken sansanin ’yan gudun hijira a Borno
Hukumar Bayar da Agaji Gaggawa ta kasa (NEMA) ta ce an kashe mutum 58 tare da raunata 78 a shekaranjiya Laraba, a wani harin kunar bakin wake a sansanin ’yan gudun hijira da ke Dikwa a Jihar Borno.Masu aikin ceto sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da ’ya gudun hijirar da ke sansanin […]
Hukumar Bayar da Agaji Gaggawa ta kasa (NEMA) ta ce an kashe mutum 58 tare da raunata 78 a shekaranjiya Laraba, a wani harin kunar bakin wake a sansanin ’yan gudun hijira da ke Dikwa a Jihar Borno.
Masu aikin ceto sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da ’ya gudun hijirar da ke sansanin wanda ke dauke da mutum dubu 50 suke layin karbar abincin safe.
Ko’odinetan Hukumar NEMA a Arewa maso Gabas, Mohammed Kanar ya ce an yi jana’izar wasu daga cikin wadanda suka rasu, yayin da aka kai wadanda suka samu rauni zuwa asibitoci.
A yammacin shekaranjiya Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwa don yi ta’aziyya ga iyalan wadanda harin na Dikwa ya shafa. “A madadin Gwamnatin Tarayya, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yana mika ta’aziyya ga iyalan wadanda harin kunar bakin wake ya shafa a sansanin ’yan gudun hijira da ke Dikwa da kuma gwamnati da daukacin al’ummar Jihar Borno,” inji sanarwa.
Mataimakin Shugaban kasar ya nuna damuwa kan yadda ’yan ta’adda marasa tausayi suka nuna tsabar muguntarsu a kan mutanen da suke gudun hijira daga muhallansu saboda miyagun tu’annatin rusa musu gidaje da suka yi. Kuma ya bayar da a bayar da cikkakken tsaro a sansanonin ’yan gudun hijira da ke sassan kasar nan don dakile sake aukuwar irin haka.