Mutum 6 sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota

Mutum shida ne suka mutu wasu 11 kuma suka ji rauni a wani hatsari da ya rutsa da motar bus da wata tirela. Rahotanni sun ce motocin biyu sun yi taho mu gama ne a hanyar Nteje-Onitsha a Jihar Anambra ranar Lahadi. Shaidu sun ce an kai gawarwakin wadanda suka mutun dakin ajiye gawa na […]

Mutum 6 sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota

Wani hatsarin nota da ya auku a Jihar Anambra

Hoto: NAN

Mutum shida ne suka mutu wasu 11 kuma suka ji rauni a wani hatsari da ya rutsa da motar bus da wata tirela.

Rahotanni sun ce motocin biyu sun yi taho mu gama ne a hanyar Nteje-Onitsha a Jihar Anambra ranar Lahadi.

Shaidu sun ce an kai gawarwakin wadanda suka mutun dakin ajiye gawa na asibitin Iyi-Ene, Ogidi, inda ake kula da wadanda suka samu rauni.

Kakakin Kwamandan Hukumar Kare Hadura ta Kasa (FRSC) na jihar, Kamal Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin.