Mutum 6 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Kwale-kwale ya kife da kusan mutum 40 a yankin Malamawa da ke Gundumar ’Yan Dutse ta Ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa.

Mutum 6 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Mutum shida sun rasu, yayin da aka ceto mutum 15 da ransu bayan wani kwale-kwale ya kife a yankin Malamawa da ke Gundumar ’Yan Dutse ta Ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ta tabbatar da cewa an gano gawarwakin mutum shida zuwa yanzu, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da laluben sauran fasinjojin da har yanzu ba a gano ba.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne yayin da kwale-kwalen ke ɗauke da fasinjoji galibi mata da yara da ke ƙoƙarin tsallaka hanyar ruwa a yankin Malamawa.

Shi ma jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, haɗin gwiwar jami’an agajin gaggawa, da gwanayen ninƙaya daga cikin al’umma da mazauna yankin ne ya kai ga ceto mutum 15 da ransu.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da aikin ceto domin gano sauran fasinjojin da har yanzu ba a gani ba.

Hukumar SEMA ta yi kira ga al’ummomin da ke amfani da hanyoyin ruwa da su riƙa kiyaye matakan kariya da ƙa’idojin musamman guje wa ɗaukar fasinjojin da suka wuce ƙima da kuma amfani da rigunan kariya (life jackets), domin rage aukuwar irin waɗannan haɗurra.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami, yayin da iyalan waɗanda har yanzu ba a gano ba ke ci gaba da jiran sakamakon aikin bincike da ceto.