Mutum 6 sun rasu a harin ƙunar baƙin wake a Borno — ’Yan Sanda

Majiyoyi daga yankin sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana.

Mutum 6 sun rasu a harin ƙunar baƙin wake a Borno — ’Yan Sanda

Aƙalla mutum shida ne suka mutu, yayin da wasu 15 suka jikkata a wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai a garin Gwoza da ke Jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a garin Gwoza, a ranar Asabar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa an kai harin ne a wata tashae mota da ake kira Marrarraban Gwoza.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Yusuf Lawal, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce wata mace ce ‘yar ƙunar baƙin wake ce ta kai harin.

Lawal ya ce jami’in ’yan sandan shiyya na Gwoza ne, ya sanar da shi cewa aƙalla mutum shida ne suka mutu, inda aka kai wasu 15 zuwa asibiti.

Wani ganau mai suna Buba, ya shaida wa NAN cewa ’yar ƙunar baƙin waken ta yi niyyar tayar da bam ɗin ne a wajen wani biki.

Buba, ya ce harin ya jefa mutanen da suka halarci bikin cikin baƙin ciki maimakon farin ciki, inda da dama suka koma zaman makoki.

Wani ganau mai suna, Muhammed Kasim, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana.

“Mun ji ƙarar fashewar wasu abubuwa, sai ƙura ta tashi sai muka ga gawarwaki a ƙasa.”

Ya ce an kwashe mutane da dama da lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti, yayin da aka tura jami’an tsaro yankin.