Mutum 6 sun rasu a rikicin shi’a da sojoji a Abuja

Rahotanni na bayyana cewa, an kashe mutum shida da raunata mutum goma a wani rikici da ya faru tsakanin sojojin Najeriya da mabiya akidar Shi’a a garin Zuba da ke Abuja. Rikicin ya fara ne lokacin da ‘yan shi’an ke gudanar da tattaki na kawanaki arba’in na bayan Ashura. A cewar sojojin lamarin ya faru […]

Mutum 6 sun rasu a rikicin shi’a da sojoji a Abuja

Rahotanni na bayyana cewa, an kashe mutum shida da raunata mutum goma a wani rikici da ya faru tsakanin sojojin Najeriya da mabiya akidar Shi’a a garin Zuba da ke Abuja.

Rikicin ya fara ne lokacin da ‘yan shi’an ke gudanar da tattaki na kawanaki arba’in na bayan Ashura.

A cewar sojojin lamarin ya faru ne lokacin da suke rakiyar kayan aikin soji daga Abuja zuwa Kaduna inda ‘yan shi’an suka farwa sojojin a gadar Zuba.