Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Mutane da yawa sun taru domin ɗiban mai duk da ƙoƙarin da aka yi na hana su.

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Aƙalla mutane 60 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata motar dakon mai ta kife, ta kuma zubar da mai da kafin daga bisani ta fashe a Jihar Neja.

Lamarin kamar yadda rahotanni suka tabbatar ya faru a ne kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wanda ke a Jihar Neja.

A cewar Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) shiyyar Neja, Kumar Tsukwam, akasarin waɗanda abin ya rutsa da su talakawa ne mazauna yankin da suka yi gaggawar ɗiban man da ya zube bayan motar ta kife.

“Mutane da yawa sun taru domin ɗiban mai duk da ƙoƙarin da aka yi na hana su,” inji Tsukwam a cikin wata sanarwa.

“Kwatsam, sai motar tankar ta kama wuta, ta kuma kona wata motar dakon mai, ya zuwa yanzu an kwashe gawarwaki 60 da aka gano a wurin.”

Gwamnan Umaru Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa a sanarwar da sakataren watsa labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar.

A watan Oktoban shekara 2024 da ta gabata aƙalla mutum 140 ne suka mutu sakamamon konewar da suka yi lokacin da wata babbar motar ɗaukan mai ta kama da wuta a Jihar Jigawa.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS