Mutum 62 sun mutu a harin Isra’ila a tsakiyar Gaza

An kawar da ‘yan ta’addar Hamas da yawa a hare-haren da aka kai a cewar dakarun IDF.

Mutum 62 sun mutu a harin Isra’ila a tsakiyar Gaza

Harin da Isra’ila ta kai a tsakiyar Gaza ya kashe kimanin mutane 62 ciki har da mata da ƙananan yara, a cewar wasu majiyoyin kiwon lafiya a yankin Falasɗinu.

Dakarun tsaron Isra’ila (IDF) sun ce suna gudanar da bincike.

Tun da farko dai, IDF ta ce ta fara kai hare-hare a al-Bureij da ke tsakiyar Gaza da kuma yankunan gabashin Deir al-Balah a ranar Talata.

Rundunar ta IDF ta kai hare-hare ta sama kan sansanonin soji da ma’ajiyar makaman Hamas, da kuma kayayyakin more rayuwa na ƙarƙashin ƙasa mallakar Ƙungiyar Islama ta Falasɗinu  a Hamas.

“An kawar da ‘yan ta’addar Hamas da yawa a hare-haren da aka kai,” in ji IDF.

A baya dai an girke sojojin Isra’ila a al-Bureij a farkon wannan shekara, amma daga baya suka janye daga yankin.

Sai dai har yanzu Hamas na nan a yankin mai yawan jama’a, in ji IDF.

Mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke maƙwabtaka da al-Bureij da al-Maghazi sun sanar a ranar Laraba cewa an kai hare-hare ba tare da sassautawa ba a yankin.