Mutum 717 sun musulunta a Bauchi

Mutane 717 sun musulunta a kananan hukumomin Toro da Ganjuwa da ke Jihar Bauchi. Shugaban Kwamitin Kula da Sababbin Musulunta a yankin Toro Alhaji Sani Arab Tilde ne ya shaida wa wakilinmu haka.Ya ce mutanen da suka musulunta a wannan karo sun fito daga Nabordo da Tulai da Jameri a karamar Hukumar Toro sai Miya […]

Mutum 717 sun musulunta a Bauchi

LONDON, ENGLAND – FEBRUARY 18: The Sultan of Sokoto, Mohamed Sa’ad Abubakar waits to meet Prince Charles, the Prince of Wales at Clarence House on February 18, 2009 in London. The Sultan is the titular ruler of Sokoto in northern Nigeria. He is the leader of approximately 70 million Nigerian and West African Muslims and […]

 Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad AbubakarMutane 717 sun musulunta a kananan hukumomin Toro da Ganjuwa da ke Jihar Bauchi. Shugaban Kwamitin Kula da Sababbin Musulunta a yankin Toro Alhaji Sani Arab Tilde ne ya shaida wa wakilinmu haka.
Ya ce mutanen da suka musulunta a wannan karo sun fito daga Nabordo da Tulai da Jameri a karamar Hukumar Toro sai Miya da Luntu a karamar Hukumar Ganjuwa. Ya ce kwamitin ya taimaka wa marayu da nakasassu da sababbin musulunta da abinci da kuma kayan bukata na Naira dubu 248, kuma mutanen yankin suka taimaka. Don haka ya yaba musu tare da cewa har yanzu kofa a bude take wajen taimaka wa mutanen.
A wani labarin Shugaban Kwamitin Riko na karamar Hukumar Toro, Barista Aliyu Ibn Idris Tilde ya ja hankalin jama’ar yankin su taimakawa wadanda ambaliya ta lalata gonakinsu ko ta rusa gidajensu, kafin tallafin gwamnati ya isa gare su. Shugaban ya yi kiran ne a lokacin da ya zagaya yankunan da ambaliyar ta shafa da suka hada da Nabordo da Takabundu da Rimiin-Zayem da Miya-Barkatai da Tilde da Diriko da Tumu da Jimpi da Ribina da Kogin-Sallah.
Ya kirayi jama’ar yankin su nisanci gini ko zuba shara a magudanun ruwa kuma su rika tsabtace muhallinsa domin kauce wa kamuwa da cututtuka.