Mutum 75,000 ne suka nuna sha’awa ga shirin noma na APPEALS
Akalla mutum dubu 75 ne suka nuna sha’awar yin noma ta hanyar neman tallafi a shirin inganta noma na Bankin Duniya (APPEALS) a Jihar Kaduna. Da yake jawabi ga masu neman tallafin da aka gayyato don a tantance su, Ko-odinetan Shirin na Kasa, Dokta Salisu Garba, ya ce daga cikin wadanda suka nuna sha’awar shirin, […]
Akalla mutum dubu 75 ne suka nuna sha’awar yin noma ta hanyar neman tallafi a shirin inganta noma na Bankin Duniya (APPEALS) a Jihar Kaduna.
Da yake jawabi ga masu neman tallafin da aka gayyato don a tantance su, Ko-odinetan Shirin na Kasa, Dokta Salisu Garba, ya ce daga cikin wadanda suka nuna sha’awar shirin, mutum dubu 45 aka tantance inda aka fitar da mutum dubu 2,885 wadanda daga cikinsu ne za a fitar da mutum dubu 1,700 da za su amfana da tallafin.
Ya ce wadanda suka samu nasara za a karbi bayanansu da za a a ajiye a sashen tanada bayanai na APPEALS da kuma Bankin Duniya.
“Wannan sabon shirin noman kasuwanci ne kuma jihohi shida ne za su amfana da shirin da suka hada da Legas da Kuros Riba da Enugu da Kaduna da Kano sai kuma Jihar Kogi. Amma fa Jihar Kaduna ce ta fi yawan masu neman tallafin,” inji shi.
Ko-odinetan ya ce an ware kashi biyar na yawan mutanen da za a bai wa tallafin ga nakasassu wanda hakan ke nuna nakasassu 85 ne za su amfana.
Shugabar Sashen Mata da Matasa na shirin APPEALS, Ronke Akanni, ta ce za a yi wa masu neman tallafin tambayoyi ne daga nan za su fitar da tsarin shirin da suke son a ba su tallafi a kai.
Ta bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi alkawarin bayar da tallafi ga shirin na APPEALS kafin wa’adin shirin ya kare nan da shekara shida masu zuwa.
Shugaban Shirin APPEALS na Jihar Kaduna, Dokta Aminu Yahaya, ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna na sha’awar shirin APPEALS ne saboda zai inganta samar da abinci da kuma inganta tattalin arziki tare da samar da aikin yi, sannan zai janyo masu zuba jari tare da inganta rayuwar mutane, musamman manoma.