Mutum 8 sun mutu da raunata 7 a hadarin tankar mai a Kogi
Mutum takwas sun mutu yayin da bakwai suka samu mummunan raunuka lokacin da wata tirelar man fetur ta afkawa wasu motoci a babbar hanyar Lokoja babban birnin jihar Kogi zuwa Abuja a safiyar yau Litinin. Hadarin ya faru ne a unguwar Felele da ke hanyar Lokoja zuwa Abuja, inda ya rutsa da babura mai kafa […]
Mutum takwas sun mutu yayin da bakwai suka samu mummunan raunuka lokacin da wata tirelar man fetur ta afkawa wasu motoci a babbar hanyar Lokoja babban birnin jihar Kogi zuwa Abuja a safiyar yau Litinin.
Hadarin ya faru ne a unguwar Felele da ke hanyar Lokoja zuwa Abuja, inda ya rutsa da babura mai kafa uku (Keke Napep) guda hudu sai babura biyu da kananan motoci uku da wata motar basa daya, sanadiyyar kaucewar birkin tirelar.
Wani ganau mai suna Moses Johnson, ya bayyanawa wakilinmu cewa, hadarin ya faru ne da misalin 8:45 na safiyar yau, kuma wadanda suka rasa rayukan nasu sun fita ne don neman abin kari sai hadarin ya rutsa da su a wajen.