Mutum 80 sun mutu a turereniyar karbar kayan Sallah
Lamarin ya faru ne bayan daruruwan mutane sun je karbar tallafin kayan karamar sallah.
An shiga juyayi bayan mutuwar mutum 80 ciki har da kananan yara a yayin turereniyar rabon kayan Sallah a kasar Yemen.
Mayakan Houthi da ke iko da Sanaa, babban birnin kasar sun tabbatar da aukuwar lamarin a yankin Bab al-Yemen da ke birnin, inda daururwan mutane sun yi cikar kwari don karbar tallafin kayan karamar sallah.
- Gidauniya Ta Dinka wa Marayu 103 Kayan Sallah A Gombe
- Matashin da ya je Masallacin Kudus a kafa daga Faransa
Jami’an lafiya da mayakan nan Houthi sun ce an kai wadanda suka samu raunuka a turmutsutsun zuwa asibiti.
Hotuna da aka ya da a kafofin sada zumunta bayan aukuwar lamarin sun nuna mutane a kwakkwance.
Gwamnatin Yemen sun ce an tsare wasu attajirai biyu da suka dauki nauyin rabon kayan tallafin a wata makaranta.