Mutum 9 sun mutu a hadarin mota a Kano

Akalla mutum 9 ne suka rasa rayukan su yayin da mutum 15 suka samu raunuka a hadarin mota da ya faru a  kauyen Dinyar Madiga da ke karamar hukumar Takai ta jihar Kano. Jami’in sadarwa na karamar hukumar Nasiru Abu Faragai ya ce, hadarin ya faru ne tsakanin motar bas kirar Sharon mai lamba BUJ […]

Mutum 9 sun mutu a hadarin mota a Kano

Akalla mutum 9 ne suka rasa rayukan su yayin da mutum 15 suka samu raunuka a hadarin mota da ya faru a  kauyen Dinyar Madiga da ke karamar hukumar Takai ta jihar Kano.

Jami’in sadarwa na karamar hukumar Nasiru Abu Faragai ya ce, hadarin ya faru ne tsakanin motar bas kirar Sharon mai lamba BUJ 389 AA-Jigawa da kuma mota kirar Toyota Sienna mai lamba YLA 389 PK-Adamawa.

Faragai ya kara da cewa, direban Sharon din ya taso ne daga Jos zuwa Kano yayin da yazo kauce wa rami sai kauce hanya ya afkawa motar Toyota Sienna da ta taso daga Kano zuwa Yola.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta