Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
Hukumomi sun wayar da kan al’umma game da muhimmancin ɗaukar matakan kariya.
Aƙalla mutum tara ne suka rasu, yayin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 17 ya kife a Jihar Jigawa.
Yawancin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ’yan mata ne.
- Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
- Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres
Lamarin ya faru ne da ranar yammacin Lahadi, 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwalen ya taso daga ƙauyen Digawa a Ƙaramar Hukumar Jahun zuwa ƙauyen Zangon Maje da ke Ƙaramar Hukumar Taura.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Ofishin NEMA na Kano, ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin.
Wasu mazauna yankin sun ceto mutum takwas da ransu, sai dai an yi rashin sa’a mutum tara sun riga mu gidan gaskiya.
NEMA tare da haɗin gwiwar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (JSEMA), Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIWA), da jami’an Ƙaramar Hukumar sun wayar da kan al’umma kan muhimmancin bin ƙa’idojin tsaro yayin tafiya a ruwa.
NIWA, ta kuma raba wa mutanen yankin rigunan kariya na ruwa don kare kansu daga irin wannan hatsari.