Mutum 900 sun warke daga COVID-19 a Legas

Mutanen da sauka warke daga annobar coronavirus sun kai 908 bayan an sallami karin mutum 33 a jihar Legas. Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da haka bayan sallamar karin mutum 33 a jihar ranar Talata. 30 daga cikin wadanda aka sallama ‘yan Najeriya ne, sauran ukun kuma ‘yan kasar Indiya. Coronavirus: Adadin wadanda […]

Mutum 900 sun warke daga COVID-19 a Legas

Daga tsakiya a can kuryar, gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu tare da jami’an kiwon lafiya a sabuwar cibiyar killace masu coronavirus ta Oniru a Legas

Mutanen da sauka warke daga annobar coronavirus sun kai 908 bayan an sallami karin mutum 33 a jihar Legas.

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da haka bayan sallamar karin mutum 33 a jihar ranar Talata.

30 daga cikin wadanda aka sallama ‘yan Najeriya ne, sauran ukun kuma ‘yan kasar Indiya.

21 daga cikinsu an sallame su ne daga cibiyar kula da masu cutar da ke Onikan.
9 kuma an sallame su ne daga cibiyar Eti-Osa (LandMark), 2 a Lekki sannan mutum 1 daga cibiyar da ke Gbagada.

Zuwa yanzu jihar Legas ita ce kan gaba a fadin Najeriya da masu cutar COVID-19 5,277.