Mutum 9,227 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Najeriya — FRSC

Hukumar Kiyaye Haddurra ta Kasa (FRSC) ta ce hadurra 19,787 da mace-mace 9,227 aka samu a titunan Najeriya a tsakanin shekarar 2021 da 2022. Shugaban Hukumar, Dauda Biu, ya ce alkaluman da hukumar ta tattara sun nuna daga watan Janiru zuwa Disambar 2021 hadurra 10,304 aka samu a fadin Najeriya. A shekarar 2022 kuma an […]

Mutum 9,227 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Najeriya — FRSC

Hukumar Kiyaye Haddurra ta Kasa (FRSC) ta ce hadurra 19,787 da mace-mace 9,227 aka samu a titunan Najeriya a tsakanin shekarar 2021 da 2022.

Shugaban Hukumar, Dauda Biu, ya ce alkaluman da hukumar ta tattara sun nuna daga watan Janiru zuwa Disambar 2021 hadurra 10,304 aka samu a fadin Najeriya.

A shekarar 2022 kuma an samu 9,483 wanda hakan ke nuna samun raguwar kashi takwas cikin 100 idan aka kwatanta da 2021.

Ya bayyana wa manema labarai ranar Litinin a Abuja cewa hukumar za ta jibge jami’ai 36,224 da kuma kayan aikin sintiri 1,226, domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa a lokacin bukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

“Wadannan hanyoyi sun hada da na Legas zuwa Ibadan, da Abuja zuwa Kano, da Nyanya zuwa Maraba, da sauran manyan hanyoyi,“ in ji shi.

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya

’Yan bindiga sun kashe Limami da wasu a Sakkwato

Gwamnati za ta mayar da yara 5,000 makaranta a Jigawa