Mutum 994 ne suka rasu a hadura a Abuja a 2020 —FRSC

Sai dai hukumar ta ce an samu ragin wanda suka mutum, idan aka kwatanta da shekarar 2019.

Mutum 994 ne suka rasu a hadura a Abuja a 2020 —FRSC

Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC), reshen Birnin Tarayya, Gora Wobin, ya ce mutane 994 sun rasu a hadura daban-daban a 2020.

Wobin ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillacin Labarai NAN, a ranar Litinin.

“Idan aka duba yawan haduran da aka samu a 2020 da 2019, za a ga a 2020 ya sauka da kashi 14%.

“Daga cikin mutune 4,532 da suka yi hadari a 2020 mutane 201 ne suka rasu, a 2019 kuma mutane 248 ne suka rasu, an samu ragin kashi 18%.

“Mutum 1,728 kuma ne suka ji rauni a 2020, sabanin 2019 inda aka samu mutum 2,385.

“Mutane 2, 603 sun tsirage a haduran na 2020, yayin da a 2019 kuma 3,375 suka tsallake rijiya da baya,” cewar Wobin.

Ya bayyana cewa abubuwan da ke kawo hadura a Abuja sun hada da gudun da ya saba ka’ida, daukar kaya fiye da kima da sauransu.