Mutum biyar sun mutu a hadarin jirgin kasa a Legas
Hadarin jirgin kasa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar a safiyar yau Talata a hanyarsa ta zuwa jihar Ogun, cikin wadanda suka rasu akwai mai tukin babur mai taya uku tare da fasinjoji. Jirgin fasinjan ya taso ne daga tashar jiragen kasa ta Ike Aro zuwa garin Itoki jihar Ogun a hanyarsa ne ya hadu […]
Hadarin jirgin kasa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar a safiyar yau Talata a hanyarsa ta zuwa jihar Ogun, cikin wadanda suka rasu akwai mai tukin babur mai taya uku tare da fasinjoji.
Jirgin fasinjan ya taso ne daga tashar jiragen kasa ta Ike Aro zuwa garin Itoki jihar Ogun a hanyarsa ne ya hadu da babur mai taya uku wanda ta dauko fasinjoji hakan ya sa duk suka rasu sanadiyyar hadarin.
Wani ganau ya bayyanawa majiyarmu cewa, hadarin ya faru ne a tsakanin garin Agbado da tashar Iju Ishaga da ke jihar Legas.