Mutum biyu sun binne ɗan uwansu da ransa a Zariya

Ɗan uwan nasu ya sace wata wayar salula ta kimanin naira dubu 35 a wurin da suke aikin leburanci.

Mutum biyu sun binne ɗan uwansu da ransa a Zariya

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da kame wasu mutum biyu da suka yi yunƙurin kashe ɗan uwansu ta hanyar rufe shi a rami da ransa a unguwar Gauraki da ke gundumar Kufena a Ƙaramar Hukumar Zariya.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, ASP Mansur Hassan ya ce an cafke ababen zargin ne bayan da wani hoton bidiyo ya ɓulla a kafafen sada zumunta dangane da aika-aikar da suka yi na yunƙurin kashe ɗan uwansu.

Ya ce rundunar ta samu nasarar gano yaron mai suna Abubakar Aliyu mai shekaru 20 da aka binne a cikin wani kango a kauyen Gauraki.

Waɗanda ake zargin wa da ƙani ne — Yahaya Abdulkadir mai shekara 24 da Abdullahi Abdulkadir mai shekara 18 — kuma ’yan gida ɗaya ne.

Kakakin ’yan sandan ya ce duk waɗanda lamarin ya shafa leburanci suke yi a Abuja.

Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa ’yan uwan biyu suna zargin wanda suka rufe a ramin da laifin sace wata wayar salula ta kimanin naira dubu 35 a wurin da suke zaune.

Sai dai kuma sun yanke shawarar ɗaukar wannan mataki duk da cewa an sulhunta su da zummar za su riƙa cire kuɗin wayar daga cikin kuɗin sallamarsa ta aikin a duk ranar har ya gama biya.

Bayanai sun ce bayan an cimma wannan yarjejeniyar ce kuma ya gudo gida, lamarin da ya sa suka biyo shi kuma suka ɗauki wannan mataki.

Kakakin ’yan sandan ya ce lamarin ya faru a ranar Asabar, 10 ga watan Agustan, inda ababen zargin suka ɗaure masa hannu da kafafu tare da toshe masa baki sannan suka rufe shi a rami a har zuwa wuyansa.

A cewar kakakin, wani bawan Allah da ke wucewa ne ya ji kururuwarsa kuma yana leƙawa cikin kangon ya hango yaron, lamarin da ya gaggauta sanar da jama’a kuma aka ceto shi.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kaduna, AD Ali wanda ya ba da umarnin a gaggauta gurfanar da waɗanda ake zargi da zarar an kammala bincike.

Kwamishinan ya kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Boko Haram ta ƙone coci da gidaje a Borno

DAGA LARABA: Dalilan ɓaraka a tsakanin iyayen riƙo da ’ya’yan riƙo

Tsaro: Majalisa za ta ƙara Naira Biliyan 50 a kasafin ma’aikatar tsaro

Jami’ar Jihar Gombe ta rantsar da sabbin likitoci 56