Mutum biyu sun rasu a gobarar gidan mai na Kano
Mutum biyu sun rasu a wata gobara da ta tashi a gidan main a A.A Rano da ke kan titin Bompai a Kano a shekaranjiya Laraba.Gobarar ta taso ne daga wata tanka da misalin karfe 2 :00 na rana inda ta watsu zuwa wasu gine-gine da ke kusa ta jawo asarar dukiya ta miliyoyin Naira.Wani […]
Mutum biyu sun rasu a wata gobara da ta tashi a gidan main a A.A Rano da ke kan titin Bompai a Kano a shekaranjiya Laraba.
Gobarar ta taso ne daga wata tanka da misalin karfe 2 :00 na rana inda ta watsu zuwa wasu gine-gine da ke kusa ta jawo asarar dukiya ta miliyoyin Naira.
Wani ganau mai suna Ado Ahmed ya shaida wa Aminiya cewa wutar ta kama ne sakamkon kuskuren da aka samu daga mazubin man inda ya zube a kasa lamarin da ya jawo wuta ta tahi.
Sai dai wani ganau da ya nemi a boye sunansa ya ce wutar ta kama ne lokacin da ake sauke mai daga wata tankar mai sannan a ana sayar da shi a gefe.
Aminiya ta gano cewa baya ga tankar mai da wutar ta kama, wutar ta kama gaba dayan ginin gidan man da wani gini mai hawa biyu da ke makwabtaka da shi da ake kira bisa House.
Wadanda suka rasu a gobarar inji majiyarmu sun hada da direban motar da wani ma’aikacin gidan man da aka bayyana sunansa da Ali, sai wadansu da suka samu raunuka da aka kai su asibiti.
Shugaban Sashin Kula da Hadari na Hukumar Sibil Difens (NSDSC) na Jihar Kano, Alhaji Abdulhamid Salisu ya ce suna samun kiran gagagwa suka isa wurin inda suka yi kokarinsu tare da jami’an kwana-kwana wajen kashe gobarar da hana batagari kwasar ganima.