Mutum daya ya mutu a yamutsin ’yan kungiyar OPC da ’yan sanda a Legas
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mutum daya da raunata wani dan sanda a lokacin da ’yan sanda suka yi ba-ta-kashi da ’yan kungiyar Yarabawa Zalla (OPC) a ofishin ’yan sanda da ake unguwar Ajegunle.Aminiya ta gano cewa daya daga cikin ’yan kungiyar OPC din da ya rasa ransa sunansa Dauda Apampa, […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mutum daya da raunata wani dan sanda a lokacin da ’yan sanda suka yi ba-ta-kashi da ’yan kungiyar Yarabawa Zalla (OPC) a ofishin ’yan sanda da ake unguwar Ajegunle.
Aminiya ta gano cewa daya daga cikin ’yan kungiyar OPC din da ya rasa ransa sunansa Dauda Apampa, shi kuwa dan sandan da ya sami rauni sakamakon harbin bindiga sunansa Kofur Emeka, kuma hargitsin ya tashi ne sakamakon rashin jituwar da aka samu kan sakin wani mutum mai suna Adebayo daga hannun ’yan kungiyar OPC.
Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa da bai so a bayyana sunanasa ba, saboda dalilan tsaro, ya ce ’yan kungiyar OPC sun kama Adebayo kan zargin yi wa wata budurwa fyade a ranar Juma’ar da ta gabata, sai ’yan sanda suka je inda ’yan OPC suke tsare da shi suka kubutar da shi karfi da yaji.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas, Ngozi Braide ta bayyana cewa tuni aka kame dan sandan da ake zarginsa da yin harbin da ya yi sanadin mutuwar dan OPC.
Ta bayyana cewa tuni har an riga an fara bincike don gano gaskiyar lamarin da tabbatar da adalci.
Ta ce, “An kai wa ’yan sandan hari ne shi ne su kuma suka mayar da martani don kare kansu daga wadanda suka kai musu harin. dan sandan da ya yi harbin da ya janyo kisan, an kama shi sannan kuma ’yan OPC sun harbi wani kofur, amma yana murmurewa a asibiti, kuma kura ta lafa, sannan an dauki matakan tsaro don hana sake aukuwar lamarin”.
To sai dai daya daga cikin shugabannin kungiyar OPC na Jihar Legas, Wasiu Afolabi ya zargi ’yan sanda da fara kai hari ga yaransa.
Ya ce, “’yan kungiyarmu sun kama mutumin kan zargin yi wa yarinyar fyade, amma sai ’yan sanda suka zo suna harbi da bindiga suka sa aka sake shi karfi da yaji. Da muka je wurin don tattaunawa da su sai kawai suka bude mana wuta har suka kashe mana mutum daya”.