Mutum daya ya tsira a hadarin jirgin saman Aljeriya

Jirgin sojan Aljeriya da ya yi hadari ya halaka mutum 77 cikin mutum 78 da ke cikinsa. Mutum daya ya tsira a wannan hadarin jirgin saman. Jirgin samfurin C-130 Hercules ya fado ne a yankin Oum El Bouaghi, inda ya dauki fasinjoji 74, tare da sojoji da iyalansu, da matukan jirgin, kamar yadda ma’aikatar yada […]

Mutum daya ya tsira a hadarin jirgin saman Aljeriya

Jirgin sojan Aljeriya da ya yi hadari ya halaka mutum 77 cikin mutum 78 da ke cikinsa. Mutum daya ya tsira a wannan hadarin jirgin saman. Jirgin samfurin C-130 Hercules ya fado ne a yankin Oum El Bouaghi, inda ya dauki fasinjoji 74, tare da sojoji da iyalansu, da matukan jirgin, kamar yadda ma’aikatar yada labarai ta kasar ta bayyana.
Tuni masu aikin ceto suka gano gawarwakin mutum 76, a inda jirgin ya yi hadar; gawarwakin dai sun hada da wasu mata hudu. Shi kuwa wand aya tsira a wannan hadari, yana can kwance a asibitin sojoji da ke irnin Constantine da ke gabashin Babban birnin kasar, wato kimanin kilomita 2300 daga Aljirs, kamar yadda rediuyon al’ummar kasar ya bayar da rahotanni.
Jirgin day a yi hadarin ya tashi ne daga saharar Tamanrasset don zuwa Kudancin Constantine, wato kilomita 320 a gabas da birnin Aljirs. Jirgin dai ya rasa samun sakonnn sadarwa a tsakaninsa da tashar jiragen saman kasar.