Mutum dubu 21,878 ke neman gurbin aikin ‘yan sanda 10,000 a kwana 5

Hukumar gudanarwan ‘yan sandan Najeriya ta ce, a yanzu haka kimanin mutum dubu 21,878 suka tura takardun neman aikin dan sanda a cikin kwanaki biyar na guraben mutum dubu 10 da ake bukata a hukumar, ranar Juma’a 30 ga Nuwamba 2018. Kakakin hukumar ‘yan sandan Ikechukwu Ani ya ce, an samu adadin masu neman aikin […]

Mutum dubu 21,878 ke neman gurbin aikin ‘yan sanda 10,000 a kwana 5

Hukumar gudanarwan ‘yan sandan Najeriya ta ce, a yanzu haka kimanin mutum dubu 21,878 suka tura takardun neman aikin dan sanda a cikin kwanaki biyar na guraben mutum dubu 10 da ake bukata a hukumar, ranar Juma’a 30 ga Nuwamba 2018.

Kakakin hukumar ‘yan sandan Ikechukwu Ani ya ce, an samu adadin masu neman aikin ta hanyar duba manhajar neman aikin ta intanet a jiya Talata. An samu adadin maza dubu 20,217 da kuma mata dubu 1,661 masu neman aikin.