Mutum dubu 40 na neman afuwa ga karen da ya yayyage fuskar yaro a Amurka
Wani kare da ya yayyage fuskar wani yaro dan shekara hudu a Phoenid ta Jihar Arizona a Amurka ya samu dubban mutane da ke neman kotu ta yafe masa ta hanyar kamfe a Facebook a daidai lokacin da kotun ke shirin yanke hukunci kan makomar karen. Kamfanin Dillancin Labarai na AP, wanda ya ruwaito labarin ya […]
Wani kare da ya yayyage fuskar wani yaro dan shekara hudu a Phoenid ta Jihar Arizona a Amurka ya samu dubban mutane da ke neman kotu ta yafe masa ta hanyar kamfe a Facebook a daidai lokacin da kotun ke shirin yanke hukunci kan makomar karen.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP, wanda ya ruwaito labarin ya ce alkalin kotun birnin yana iya yanke hukunci a ranar Talata 25 ga Maris, kan ko za a iya kashe karen mai suna Mickey, wanda ya cicciji yaron mai suna Kebin bicente a fuska, wanda kuma likitoci suka ce zai dauki watanni ko shekaru ana yi masa tiyatar gyaran fuskar.
Tun ranar 20 ga Fabrairu da kare Mickey ya lahanta yaron, lamari ya zama abin surutu a shafin Facebook, inda ya samu goyon bayan mutum dubu 40 da suka rubuta takardar kuka suna neman a ceci ransa, kodayake sun ce hakan ba yana nufin sun fifita karen a kan yaron ba ne.
“Wannan ba batun tsakanin Kebin da Mickey ba ne,” inji wani lauya John Schill, wanda ke kare karen a kotu, “kashe Mickey ba zai kawo saukin radadin raunin da Kebin ya ji ba. Abin sani kawai ana shirin kashe wani rarraunan kare ne”.
Jama’a na kallon irin wannan nau’in kare mai kama da alade a matsayin hadari, matsayin da masu kaunar irin nau’in ke musantawa.
Guadalupe billa, wanda ya je inda karen ya yi wannan ta’asa ya shigar da kara yana neman a halaka karen, saboda yadda ya ga lamarin ya tuna wannan yaro na iya zama dansa, kuma ba zai so haka ta faru da wani daban ba.
Lauya Schill ya ce yana aiki ne da wata kungiya da ba ta neman riba ba mai suna The Ledus Project, da ke tara kudi domin kare dabbobin da ke fuskantar hadarin kashewa. Kuma kungiyar ta kafa asusun domin tserar da kare Mickey inda ta samu gudunmawar Dala 5,600 (kimanin Naira dubu 924) domin cimma wannan manufa.
Ya ce mai kula da Kebin ne ya kamata a dora wa laifi, ba karen ba, musammam ganin Kebin ne ya je daukar wani kashi a gaban Mickey, wanda ke daure da sarka, inda shi kuma ya auka masa.
An kwantar da Kebin a asibitin Maricopa Medical Center don jinyar raunin da ya samu a ido da mukamuki. Kuma wani likita a asibitin Mayo kuma babban likitan tiyata, Dokta Salbatore Lettieri, ya ce ya samu nasarar gyara karayar da yaron ya samu a fuska domin ba Kebin damar budewa da rufe idonsa, amma har yanzu ba zai iya bude idon ba sai an sake yi masa aiki.
Kebin ya samu gudunmwar Dala 6,000 (kimanin Naira dubu 990) bayan da aka kafa wata gidauniya ta yanar gizo.
An ce karen ya samu goyon baya ne bayan da wani mai kula da shi a cibiyar adana dabbobi ta Maricopa County, ya rubuta wani bayani a Facebook mai cewa Mickey “zai bakunci Lahira.”
Kakakin cibiyar Melissa Gable ta ce ma’aikacin zai fuskanci ladabtarwa, amma ba ta yi karin bayani ba.