Mutum dubu 705 ke neman gurbin ’yan sanda dubu 10

Hukumar Kula da Harkokin ’Yan sanda (PSC), ta ce ta karbi takardun neman aiki dubu 705 da 352 na mutanen da ke neman a dauke su a aikin dan sanda zuwa karfe 7:30 na safiyar Talatar da ta gabata.Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa […]

Mutum dubu 705 ke neman gurbin ’yan sanda dubu 10
Mutum dubu 705 ke neman gurbin ’yan sanda dubu 10

Hukumar Kula da Harkokin ’Yan sanda (PSC), ta ce ta karbi takardun neman aiki dubu 705 da 352 na mutanen da ke neman a dauke su a aikin dan sanda zuwa karfe 7:30 na safiyar Talatar da ta gabata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar Ikechukwu Ani ya fitar a ranar Talatar a Abuja.
Sanarawar ta ce takardun neman aikin sun hada da mutum dubu 202 da 427 na masu neman a dauke su daga mukamin ASP Kadet, sai kuma dubu 169 da 446, masu neman Sufeto Kadet, yayin da dubu 333 da 479 ke neman a dauke su kurata.
Sanarwar ta ce hukumar za ta dauki ASP Kadet 500 da Sufeto Kadet 500 da ofisoshi na musamman 1,500 da kurata 7,500 domin cimma adadin dubu 10 da aka amince a dauka aikin dan sanda.
Sanarwar ta ce Shugaban Hukumar Mike Okiro, ya tabbatar da cewa hanyar da ake karbar fom-fom din tana gudana cikin nasara da gaskiya.
Mista Okiro ya tabbatar da kudirin hukumar na tabbatar da yin gaskiya wajen ganin aikin daukar ya samu nasara.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya amince a dauki ’yan sanda dubu 10 domin inganta aikinsu.