Mutum dubu 800 ke takara a kananan hukumomin Filifins
Fiye da mutum dubu 800 ke takarar shuabanci da sauran mukamai a garuruwa da kauyuka fiye da dubu 42 da ake kira barangays, a kasar Filifins, inda harkokin siyasar suka rincabe da tashe-tashen hankula da magudin zabe; haka kuma al’amuran suke kasancewa hatta a manyan zabukan kasar.Alkaluma sun nuna cewa mutum 15 suka mutu a […]
Fiye da mutum dubu 800 ke takarar shuabanci da sauran mukamai a garuruwa da kauyuka fiye da dubu 42 da ake kira barangays, a kasar Filifins, inda harkokin siyasar suka rincabe da tashe-tashen hankula da magudin zabe; haka kuma al’amuran suke kasancewa hatta a manyan zabukan kasar.
Alkaluma sun nuna cewa mutum 15 suka mutu a rikicin zaben kasar a shekarar 2010, kuma 57 aka halaka a zaben 2007, a cewar ’yan sanda. A tashin hankalin baya-bayan nan, an harbe mijin wata ’yar takara da ke neman shugabancin kauyensu, a ranar Litinin din da ta gabata, inda ake zargin abokin karawarta da ke garin Jaro da ke tsakiyar gundumar Leyte. Wani mai goyon bayan dan takara ya rasa ransa a wani artabu da aka yi da sojoji a Kudancin Gundumar Agusan del Sur, kamar yadda ’yan sanda suka tabbatar.
An fara gudanar da zabukan kananan hukumomi da wakilcin kauyuka cikin lumana a daukacin fadin Filifins, amma daga bisani tashin hankali ya kawo cikas ga masu kada kuri’u a wasu yankunan karkara, inda aka yi ta samun harbe-harbe da kisan gilla da kona rumfunan zabe, kamar yadda jami’an hukuma suka bayyana.
Sojoji da ’yan sanda sun kasance cikin shirin ko ta kwana, bayan da aka halaka ’yan takara 22 da magoya bayansu, wadanda suka mutum tun kafin a fara kada kuri’u. Tashe-tashen hankula da magudin zabe su ne babban cikas din da ke yi wa zabukan kasar Filifins illa.