Mutum fiye da miliyan 1 sun rasa matsugunni a Sudan —MDD

Yanzu haka akwai ’yan Sudan dubu 319 da ke samun mafaka a makwabta.

Mutum fiye da miliyan 1 sun rasa matsugunni a Sudan —MDD

Rikicin Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa zuwa yanzu fiye da mutum miliyan guda rikicin Sudan ya raba da matsugunansu.

MDD ta bayyana hakan ne daidai lokacin da aka shiga rana ta biyu da fara aikin yarjejeniyar tsagaita wuta, lamarin da ake zargin bangarorin da ke kaiwa juna hare-hare sun yi watsi da shi.

Wani rahoto da Hukumar Kula da Kaurar Baki ta Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar a ranar Laraba bayan tattara bayanai kan halin da ake ciki a kan iyakokin kasar, ta ce yakin ya tarwatsa dubunnan ‘yan kasar wadanda suka fantsama kasashen da ke makwabtaka da Sudan.

Rahoton ya bayyana cewa yanzu haka akwai ‘yan Sudan dubu 319 da ke samun mafaka a makwabta da suka kunshi ‘yan gudun hijira dubu 132 a Masar, sai wasu dubu 80 a Chadi kana wasu dubu 69 a Sudan ta kudu.

Baya ga wannan adadi da ke ketare, Majalisar ta ce akwai kuma wasu mutanen da yawansu ya tasamma dubu 700 wadanda ke gudun hijira a sassan Sudan bayan tserewa matsugunansu don tsira da rayukansu.

A ranar 15 ga watan da muke ciki na Afrilu ne fada ya barke tsakanin jagoran mulkin Sojin kasar Abdel Fattah al Burhan da kuma Janar Mahamat Dagalo da ke jagorantar sojojin sa kai na RSF.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin wanda zuwa yanzu ya kashe dubunnan fararen hula baya ga sojojin bangarorin biyu, har zuwa safiyar Larabar ana ci gaba da jiyo karar fashewar bama-bamai a wasu sassa na kasar.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja